Galatians 5

ʼYanci cikin Kiristi

1Saboda ʼyanci ne Kiristi ya ʼyantar da mu. Sai ku tsaya daram fa kada ku yarda ku sāke komawa ƙarƙashin nauyin bauta. 2Ku lura da kalmomina! Ni Bulus ina gaya muku cewa in kun yarda a yi muku kaciya, Kiristi ba zai zama muku da amfani ba ko kaɗan. 3Haka kuma ina ƙara sanar wa kowane mutumin da ya yarda aka yi masa kaciya cewa dole yǎ kiyaye dukan Doka. 4Ku da kuke ƙoƙarin kuɓuta ta wurin Doka an raba ku da Kiristi; kun fāɗi daga alheri. 5Amma ta wurin bangaskiya muna marmarin jira adalcin da muke bege ta wurin Ruhu. 6Gama a cikin Kiristi Yesu kaciya ko rashin kaciya ba su da wani amfani. Abin da kawai yake da amfani shi ne, bangaskiyar da take bayyana kanta ta wurin ƙauna.

7Kun yi tsere mai kyau a dā. Wa ya shige gabanku da ba za ku yi biyayya da gaskiya ba? 8Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne. 9“Ɗan yisti kaɗan ne yake gama dukan curin burodi.” 10Ina da tabbaci cikin Ubangiji cewa ba za ku bi wani raʼayi dabam ba. Wannan da yake rikita ku za a hukunta shi, ko shi wane ne. 11ʼYanʼuwa, da a ce har yanzu ina waʼazin kaciya ne, to, me ya sa ake tsananta mini har yanzu? In haka ne, ashe, an kawar da abin da yake sa tuntuɓe game da gicciye ke nan. 12Da ma a ce masu ta da hankalinku ɗin nan su mai da kansu bābānni!

13Ku ʼyanʼuwana, an kira ku ga zama ʼyantattu. Amma kada ku yi amfani da ʼyancinku don aikata ayyukan mutuntaka
Ko kuwa na jiki; haka ma a ayoyi 16, 17, 19 da 24
a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna.
14Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya cewa: “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
L Fir 19.18
15In kun ci gaba da cizo kuna kuma cin naman juna, ku yi hankali in ba haka ba za ku hallaka juna.

Rayuwa ta wurin Ruhu

16Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da shaʼawace-shaʼawacen mutuntaka ba. 17Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa ƙiyaya suke yi da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so. 18Amma in Ruhu ne yake bishe ku, ba ku ƙarƙashin Doka ke nan.

19Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke: fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; 20bautar gumaka da sihiri; ƙiyaya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, 21da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

22Amma amfanin da Ruhu yake sa shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23sauƙinkai, da kuma kamunkai. Game da irin waɗannan abubuwa babu doka. 24Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma shaʼawace-shaʼawacensa. 25Da yake muna rayuwa ta Ruhu, bari mu ci gaba da alʼamuranmu ta wurin Ruhu. 26Kada mu zama masu girmankai, muna tsokana muna kuma yin ƙyashin juna.

Copyright information for HauSRK